Matthew 21

Shigar Mai Nasara

1Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma iso Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a ɗaure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa aiko da su nan da nan.”

4Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi cewa:

5“Ku ce wa Diyar Sihiyona,
‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,
mai tawaliʼu yana a kan jaki,
a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”
Zak 9.9


6Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7Suka kawo jakar da ɗan, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. 8Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. 9Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,

“Hosanna
Wani faɗi na Ibraniyanci mai maʼanar “Ceto!” Wanda ya kasance wani salon yabo; haka kuma a aya 15
ga Ɗan Dawuda!”

“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”
Zab 118.26


“Hosanna a cikin sama!”
10Saʼad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”

11Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”

Yesu a Haikali

12Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. 13Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan adduʼa,’
Ish 56.7
amma kuna mai da shi ‘kogon ʼyan fashi.’
Irm 7.11


14Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 15Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.

16Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da yaran nan suke faɗi?”

Yesu ya amsa, ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa,

“ ‘Daga leɓunan yara da jarirai
ka shirya wa kanka yabo’
Zab 8.2
?”
17Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.

Itacen Ɓaure Ya Yanƙwane

18Washegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. 19Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ʼyaʼya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.

20Saʼad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”

21Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku’, sai yǎ faru. 22In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin adduʼa.”

An Tuhumi Ikon Yesu

23Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”

24Yesu ya amsa, ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 25Baftismar Yohanna-daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?”

Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’
26In kuma muka ce, ‘Daga mutane’— muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”

27Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”

Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”

Misali na ʼYaʼya Biyu Maza

28“Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ʼyaʼya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’

29“Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.

30“Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa, ya ce, ‘Zan tafi, ranka yǎ daɗe,’ amma bai tafi ba.

31“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?”

Suka amsa, “Na farin.”

Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.
32Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yǎ nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

Misali na ʼYan Haya

33“Ku saurari wani misali: An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Saʼan nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya. 34Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ʼyan hayan, su karɓo masa ʼyaʼyan inabi.

35“Amma ʼyan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun. 36Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ʼyan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin. 37A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’

38“Amma da ʼyan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’ 39Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.

40“To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ʼyan hayan nan?”

41Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yǎ ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ʼyan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”

42Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi ba cewa:

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi
shi ne ya zama dutsen kusurwar gini.
Ubangiji ne ya aikata wannan,
kuma abin mamaki ne a idanunmu’
Zab 118.22, 23
?

43“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani. 44Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā ba su da aya 44.


45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.

46Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

Copyright information for HauSRK